Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire - Liberia

Liberia ta rufe kan iyakarta da Cote d’Ivoire

Kasar Liberia ta kulle kan iyakarta da kasar Cote d’Ivoire, bayan harin da aka kai wa wakilan Majalisar Dinkin Duniya masu wanzar da zaman lafiya a wani kauye wanda ya yi sandiyar mutuwar mutane da dama.

Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf.
Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf. Reuters/Finbarr O'Reilly
Talla

Hukumomin kasar ta Liberia dai sun ce masu aikin agaji ne za a ba damar ketarawa tsaknin iyakokin kasashen guda biyu.

A makon jiya ne wakilan Majalisar Dinkin Duniya ‘Yan asalin kasar Nijar guda bakwai da fararen hula goma tare da wani dan kasar Cote d’Ivoire su ka mutu a yayin da wasu dauke da makamai su ka abka musu a wani kauye da ke Kudu maso yammacin Cote d’Ivoire.

Har yanzu dai ana nan an gudanar da bincike domin gano wadanda su ka kai wannan hari kamar yadda wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya, Cif Herve Ladous ya bayyana wa ‘Yan jarida.

Gwamnatin Cote d’ Ivoire ta yi zargin maharan sun fito ne daga kasar Liberia bayan musanta zargin Liberia game da rahoton kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Human Rights watch akan dakile borin ‘Yan tawayen da ke kai hare-hare akan iyakokin kasashen biyu.

Ladous dai ya ce zai halarci wani taron bankwana da za a karrama Dakarun Majalisar Dinkin Duniy a birnin Abidjan da aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis.

A wani rahoton kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch an bayyana cewa akalla mutane 40 ne su ka rasa rayukansu a irin wadannan hare haren da masu goyon bayan tsohon Shugaban kasar Cote d’Ivoire, Luarent Gbagbo su kai tun a watan Yulin shekarar bara.

Shi da Gbagbo a yanzu haka ya na nan a tsare bayan kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ta same shi da laifuffukan da su ka keta hakkin bil’adama a lokacin da ya ki sauka daga karagar mulki bayan Allassane Ouatarra ya ka da shi a zaben da ya yi sanidiyar mutuwar mutane 3,000 a rikicin da ya biyo baya zabe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.