Isa ga babban shafi
ICC-Liberia

Kotu ta samu Charles Taylor da aikata laifukan yaki a Saliyo

Kotun Duniya ta samu tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor da laifin aikata laifukan yaki a kasar Saliyo, Laifi na farko da kotun ta samu wani tsohon shugaban kasa. A ranar 30 ga watan Afrilu ne kotun zata yanke masa hukunci bayan kwashe shekaru 6 ana tabka shari’a bisa zarginsa da aikata laifukan yaki a rikicin Saliyo tsakanin shekarar 1991 zuwa 2002.

Charles Taylor Tsohon shugaban kasar Liberia
Charles Taylor Tsohon shugaban kasar Liberia Chris Hondros/Getty Images
Talla

Gwamnatin Liberia ta nemi samun zaman Lafiya tsakanin al’ummar kasar idan aka yanke wa Charles Taylor hukunci.

Shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta yi kira ga al’ummar kasar Liberia domin gudanar da addu’a ga ci gaban kasa da samun zaman lafiya.

An zargi Charles Taylor da aikata laifukan yaki da suka shafi bada umurnin kisa da ta’addanci da keta hakkin fararen hula da yi wa mata fayde tare da tursasawa yara kanana shiga aikin Soji.

A birnin Hague ne za'a yankewa mista Taylor hukunci.

A shekarar 1997 ne aka zabi Cherles Taylor matsayin shugaban kasa a Liberia, bayan shekaru biyu ne rikici ya barke a tsakaninshi da Saliyo kafin ya nemi mafaka a Najeriya.

Mista Taylor ya dade a Najeriya har zuwa shekarar 2006, kafin Najeriya ta amsa kiran kasashen duniya da suka bukaci a mika shi domin fuskantar shari'a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.