Isa ga babban shafi
Liberia

Sirleaf ta karbi rantsuwar mulki a Liberia

A jiya Litinin aka rantsar da shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf wa’adi na biyu, sakamakon nasarar da ta samu a zaben da aka yi bara. Kuma babban mai adawa da ita ya amince da zaben shugabar. Gwamnatin kasar Amurka ta yi alkalin taimakwa gwamnatin Sirleaf wajen bunkasa Demokradiya da 'Yancin Mata a ziyarar da Hillary Clinton ta kai a kasar.

Bukin Rantsar da Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf.
Bukin Rantsar da Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf. Reuters / Larry Downing
Talla

Shugaban adawar kasar, Winston Taubman, ya amince da Sirleaf a matsayin zababbiyar shugabar kasa, bukin rantsar da shugabar ya samu halartar shugabanin kasashe kimanin 35, cikinsu har da Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton.

03:59

Dr Hudu Ayuba a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria

Bashir Ibrahim Idris

A cewar Tubman, tun kammala zabe ne jam’iyyarsa ke tattaunawa da gwamnati domin warware rashin jituwar da ke tsakaninsu. Kuma bayan kwashe lokaci suna tattaunawa yanzu sun amince da hada hannu da gwamnati domin ci gaban kasa.

Jam’iyyar Tubman ta CDC yanzu haka ta yi kiran magoya bayanta dakatar da duk wata zanga-zanga da aka shirya gudanarwa a ranar rantsar da Sirleaf.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.