Isa ga babban shafi
Tunisia

Kotun Tunisia ta yanke wa Ben Ali hukuncin daurin shekaru 20

Wata koton Soji a kasar Tunisia ta yanke wa tsohon shugaban kasar Zine al-Abidine Ben Ali hukuncin daurin shekaru 20 a gidan Yari amma ba a gaban idonsa ba, bayan kama shi da laifin haddasa rikici a lokacin da ‘Yan sanda suka yi kokarin ficewa da wani dansa daga Tunisia.

Tsohon shugaban Tunisia Zine al-Abidine Ben a lokacin da yake jwabi ta kafar Telebijin bayan barkewa zanga-zangar adawa da gwamnatin shi
Tsohon shugaban Tunisia Zine al-Abidine Ben a lokacin da yake jwabi ta kafar Telebijin bayan barkewa zanga-zangar adawa da gwamnatin shi REUTERS/Tunisian Television/HO
Talla

Ben Ali wanda ya samu mafaka a Saudiya bayan barkewar zanga-zangar adawa da gwamnatin shi a ranar 14 ga watan Janairu, tuni kotu ta yanke masa hukuncin dauri shekaru a gidan Yari akan tuhume tuhumen da suka da hada Cin hanci da gallazawa mutane.

A watan jiya ne kotun Sojin kasar ta bukaci a yanke wa Ben Ali hukuncin Kisa bisa rawar da ya taka wajen bada umurnin murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shi.

Har yanzu dai a kasar Tunisia babu wani Jami’in Gwamnatin Ben Ali da aka kama da laifi game da mutuwar masu zanga-zanga 300 al’amarin da yasa dangin mamatan ke kira ga bangaren shari’a aiwatar da adalci.

Tunisia ita ce kasa ta farko da zanga’zangar adawa da gwamnati ta fara barkewa a kasashen Larabawa, kafin zanga-zangar ta yadu zuwa Masar da Yemen da Libya da Syria da Bahrain inda zanga-zangar ta yi awon gaba da Hosni Mubarak da Kanal Gaddafi da kuma Ali Abdallah Saleh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.