Isa ga babban shafi
Kenya

Mutane 11 sun mutu a kisan ramuwar gayyar kasar Kenya

Akalla mutane 11 ne su ka mutu a kisan da wasu ‘Yan bindiga su ka yi wanda ake ganin na ramuwar gayyar ne na wasu mutane 52 da aka kashe a watan jiya.

Yankin Tana Rivers, da kabilun Pokomo da Orma a Kenya ke rikici a kai
Yankin Tana Rivers, da kabilun Pokomo da Orma a Kenya ke rikici a kai Photo AFP/Simon Maina
Talla

A cewar hukumar ba da agaji ta Red Cross, wasu mutane 10 kuma sun sami raunuka a harin wanda aka kai shi a yankin Tana River da ke kasar ta Kenya.
 

“Akwai tashin hankali sosai a yankin” inji wata jami’ar Red Cross, Nelly Muluku, a hirarsu da Kamfanin Dillancin labaran AFP.
 

A watan jiya ne aka kashe mutane 52 a wani rikicin ‘Yan kabilar Pokomo da Orma wadanda ke takaddama akan filaye da ruwa.

‘Yan kabilar Pokomo, dai mafi yawansu manoma ne da ke shuka kusa da tafki a yayin da su kuma ‘Yan Orma makiyaya ne.
 

A shekarar 2001, akalla mutane 130 aka kashe a rikici daba daban a yankin kuma tsakanin kabilun biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.