Isa ga babban shafi
Kenya

‘Yan sanda Biyu sun mutu a Zanga-zangar kasar Kenya

An samu mutuwar ‘Yan Sanda guda Biyu a zanga-zangar da matasa ke yi a birnin Mombasa na kasar Kenya bayan kai wani harin gurneti. Jami’an tsaro a kasar suna kokarin kwantar da zanga-zangar da aka shiga kwanaki biyu bayan kashe wani malamin addini Aboud Rogo Mohammed.

'Yan Sandan kasar Kenya suna fito na fito da masu Zanga-zanga
'Yan Sandan kasar Kenya suna fito na fito da masu Zanga-zanga
Talla

Zanga zangar a jiya Talata ta yi sanadiyyar mutuwar wani Dan Sanda tare da raunata wasu da dama, bayan da aka harba gurneti a motar ‘Yan Sandan.

Ofisoshin jakadancin kasashen waje, da suka hada da Faransa da Australia da Birtaniya, sun gargadi turawan kasarsu gujewa yin tafiya zuwa birnin na Mombasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.