Libya
An yi musayar wuta tsakanin dakarun Libya da magoya bayan Gaddafi
Wasu ‘Yan bindiga a Libya, sun kai hari kan magoya bayan Tsohon shugaba Marigayi Kanal Muammar Ghaddafi a garin Bani Walid, inda aka kashe mutane 11 tare da raunana wasu da dama. Harin na zuwa ne a dai dai lokacin da ake cika shekara da karbe birnin Bani Walid daga ikon Gaddafi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Wani jami’I a Bani Walid ya shaidawa kamfanin dillancin labaran faransa cewa, ta shiyoyi uku aka dingi kai wa garin hari da makaman roka.
Abdullahi al Mansuri, mataimakin Daraktan asibitin garin, yace sun karbi gawawwaki Bakwai da wadanda suka samu raunuka 75.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu