Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Jam’iyar adawar DA a Afrika ta Kudu ta yi babban kamu

Wani babban kusa a Jam’iyar Africa National Cpngtress a Afrika ta kudu, Nosima Balindlela, ta canja sheka zuwa babbar jam’iyar adawa ta Democratic Alliance (DA). Jam’iyar adawa ta DA ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau.Balindlela na daya daga cikin kusoshin babban kwamiti na jam’iyar ta ANC.  

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma a taron tarayyar kasashen Afrika
Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma a taron tarayyar kasashen Afrika REUTERS/Yves Herman
Talla

“Na dauki wannan mataki ne saboda na yi imanin cewa, DA itace jami’yar da ke da muradan da zata kyautata wannan kasa.” Ta ce.

Ta kara da dewa, yadda ake tafityar da mulki a kasar ta Afrika ta kudu, ba haka Nelson Mandela da Oliver Tambo ke buri a yi ba.

Masu tsokaci akan al’amuran yau da kulum na kasar Afrika ta Kudu, na nune duk da cewa Balindlela bata taka rawar gani a siyasar ta Afrika ta Kudu, ficewarta daga ANC zai zamnato wani babban rauni ne akan jam’iyar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.