Isa ga babban shafi
Masar

Masoyan Morsi sun ce sun samu nasara a zaben raba gardama

A kasar Masar an fara kidayar kuri’un zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki wanda ake takaddama a kai tsakanin shugaba Muhamed Morsi da ‘Yan adawa. Yanzu haka rahotanni sun ce an fara kidayar kuri’un a manyan biranen masar, guda biyu, birnin Al kahira da Alexandria da safiyar Lahadi.

Fadar Shugaban Masar Muhammed Morsi
Fadar Shugaban Masar Muhammed Morsi Reuters
Talla

A karshen mako mai zuwa ne za’a gudanar da zagaye na biyu na zaben.
Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Brotherhood da kafofin yada labaran masar sun ce kuri’un farko sun nuna kashi 70 cikin 100 sun jefa kuri’ar amincewa.

Sai dai kuma a bangaren ‘Yan adawa sun ce kashi 66 sun jefa kuri’ar kin amincewa da sabon kundin tsarin mulkin tare da zargin Jam’iyyar Morsi da yin magudi a zaben.

Idan dai har aka ci gaba da wannan takaddama game da sakamakon zaben to babu tantama zai haifar da tanzoma a kasar ta Masar tsakanin ‘Yan adawa da Gwamnatin Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.