Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

Rikici ya barke tsakanin Fulani da Malinke a Guinea Conakry

Akalla mutane 30 ne suka samu raunuka sakamakon barkewar wani rikici tsakanin gungu biyu na ‘yan kasuwa kafin daga bisani rikicin ya rikide ya zama na kabilanci tsakanin Fulani da kuma Malinke a yau juma’a a birnin Conakry na kasar Guinea.

'Yan sanda a birnin Conakry
'Yan sanda a birnin Conakry © AFP/Cellou Binali
Talla

Bayanai na nuni da cewa rikicin ya barke ne a wata babbar kasuwa da ke unguwar Matoto bayan tasowa daga sallar juma’a, kuma ‘yan kabilar Malinke ne suka soma kai wa Fulanin hari a cikin masallcinsu ta hanyar jifar su da duwarwatsu, sannan kuma suka ci gaba da afkawa shagunan Fulanin suna wawashewa.
Daga ranar labarar da ta gabata zuwa yau, an samu barkewar tashe-tashen hankula har sau uku a Conakry, inda tun bayan kammala zaben shugabancin kasar ake ci gaba da zaman doya da man-ja tsakanin ‘yan kabilar Malinke ta shugaba Alpha Conde da kuma Fulani wato kabilar da jagoran ‘yan adawa na kasar Cellou Dalen Diallo ya fito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.