Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Cutar HIV ta yi kamari ga matan Afrika ta Kudu

Wasu alkalumma da ma’aikatar Lafiya ta fitar a kasar Afrika ta kudu an bayyana kashi 28 na matan kasar suna dauke da cutar Sida ko HIV idan aka kwatanta da kashi Hudu na maza da ke dauke da cutar.

Matan Afrika ta kudu sun fito domin yada fatawar yaki da cutar HIV AIDS
Matan Afrika ta kudu sun fito domin yada fatawar yaki da cutar HIV AIDS Foto24/Gallo/Getty Images
Talla

Ministan lafiya Aaron Motsoaledi yace matsalar ta yi kamari ne saboda ‘Yan mata da ke alaka da masu manyan shekaru musamman masu hannu da shuni da ake kira “sugar daddies.”

Ministan yace bincikensu ya gano ‘Yan mata suna kauracewa kwanciya da samari, kamar yadda Motsoaledi ya shaidawa jaridar Sowetan, yana mai kira ga ‘Yan matan su kauracewa aikata wannan tabi’ar.

Binciken kuma yace ‘Yan matan Sakandare kimanin 94,000 suka samu ciki a 2011 yawancinsu ‘Yan shekaru 10.

Alkallumman gwamnatin kasar Afrika ta kudu ya nuna kimanin mutane miliyan 6 ke dauke da cutar HIV daga cikin al’ummar kasar Miliyan 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.