Isa ga babban shafi
Masar

Adly Mansour ya bayyana fatar mayar da Masar turbar demokuradiyya

Shugaban rikon kwaryar kasar Masar, Adly Mansour, ya yi alkawalin mayar da kasar turbar demokuradiya a farkon shekara mai zuwa bayan mutuwar mutane 51, yawancinsu magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Morsi.

Shugaban Rikon kwarya  Adly Mansour, wanda sojoji suka dora ya jagoranci Gwamnatin Masar bayan kifar da gwamnatin Morsi
Shugaban Rikon kwarya Adly Mansour, wanda sojoji suka dora ya jagoranci Gwamnatin Masar bayan kifar da gwamnatin Morsi REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Shirin ya hada da kafa kwamitin da zai sake duba kundin tsarin mulkin kasar cikin kwanaki 15 masu zuwa da kammala sauye sauye ga kundin tsarin mulki da kuma gudanar da zaben raba gardama a cikin watanni hudu da zaben ‘Yan Majalisu a farkon shekara mai zuwa, sai kuma zaben shugaban kasa da zarar sabbin ‘Yan Majalisu sun fara aiki.

Harin da aka kai wa magoya bayan jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi, shi ne ya kawo tsaikun nada sabon Firaminista, bayan wani bangare na ‘Yan adawa ya fice daga sabuwar gwamnatin ta Adly Mansour.

Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta fitar da sunayen wadanda suka mutu a harin, kuma ma’aikatar kula da harakokin cikin gida tace akwai ‘Yan sanda guda biyu da Soja guda cikin wadanda suka mutu.

‘Yan uwa Musulmi sun yi zargin Sojoji ne suka kai masu hari, amma Sojojin sun ce ‘Yan ta’adda ne suka kai harin.

Yanzu haka Jam’iyyar Morsi ta FJP ta yi shelar gudanar da babbar zanga-zanga domin juyayin mutanen da suka mutu, a harin da shugaban ‘Yan uwa musulmi ya kira a matsayin kisan kiyashi.

Kasashen duniya da dama sun yi Allah Waddai da harin, yayin da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci a gudanar da binciken gano wadanda ke da alhakin kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.