Isa ga babban shafi
Masar

An bayar da umurnin cafke jagoran ‘Yan uwa musulmi a Masar

Masu gabatar da kara a Masar sun bayar da umurnin cafke shugaban Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Brotherhood Mohamed Badie da wasu manyan jami’an jam’iyyar da ake tuhuma sun hura wutar rikicin da ya yi sanadiyar kashe mutane sama da Hamsin.

Shugaban Jam'iyyar 'Yan uwa Musulmi Mohamed Badie
Shugaban Jam'iyyar 'Yan uwa Musulmi Mohamed Badie REUTERS/Mohamed Abd El-Ghany/
Talla

Tuni aka cafke wasu manyan jiga jigan Jam’iyyar tare da bayar da sammaci cafke wasu daruruwa.

Wata majiya daga bangaren shari’a ta shaidawa kamfaninin Dillacin Labaran Faransa na AFP cewa mutane 200 ne masu gabatar da kara suke tuhuma, kuma yawancinsu magoya bayan hambararren shugaban kasa ne Mohammed Morsi.

Majiyar tace mutanen za su fuskanci bincike na tsawon kwanaki 15 akan zargin aikata laifukan kisa da hura wutar rikici da daukar makamai.

Kimanin mutane 650 ne aka cafke a rikicin ranar Litinin da ya janyo hasarar rayuka, amma an bayar da belin mutane 450.

Yawancin wadanda suka mutu magoya bayan jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ne kuma shugabannin jam’iyyar sun yi zargin jami’an tsaro ne suka kai harin da subahin safiya.

Amma rundunar sojin kasar tace ‘Yan ta’adda ne suka kai harin.

Bayar da umurnin cafke shugaban Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulimi na zuwa ne a dai dai lokacin da a ke kokarin kafa sabuwar gwamnati bayan sojoji sun hambarar da gwamnatin Morsi suka damka wa Adly Mansour alkalin kotun koli.

Kakakin jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi Gehad El-Haddad yace umurnin cafke shugabansu, wani yunkuri ne na tarwatsa magoya bayan Jam’iyyar da ke zanga-zangar neman Sojoji su mayar da Mohammed morsi a saman madafan iko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.