Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 56 suka mutu a hare haren ‘Yan bindiga a Najeriya

Wani hari da wasu ‘Yan bindiga suka kai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 44 a wani Masallaci da ke garin Konduga a Jihar Barno. An samu kuma mutuwar mutane 12 a kauyen Ngom da ke kusa da garin.

Wani Dan Banga saman taya yana gudanar da aikin binciken Motoci a garin Mafoni Jahar Borno a Najeriya
Wani Dan Banga saman taya yana gudanar da aikin binciken Motoci a garin Mafoni Jahar Borno a Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Kamfanin Dillancin labaran AP, ya ruwaito wani jami’in tsaron farin kaya da wani Dan banga na cewar, sun kirga gawawwaki 44 a Masallacin.

Dan bangan Usman Musa yace, cikin wadanda aka kashe harda jami’ansu guda hudu da suka kai dauki.

Ana sa ran an kai harin ne domin mayar da martani ga ‘Yan Banga da ke taimakawa jami’an tsaro wajen farautar ‘Yan Boko Haram.

Rahotanni sun ce ‘Yan bindiga sun bude wuta ne a cikin Masallacin na Konduga a ranar Lahadi.

Wasu Rahotannin kuma sun ce mutane 12 ne suka mutu a wani hari da ‘Yan bindiga suka kai a Ngom kusa da Mafa a ranar Assabar.

Mazauna garin Konduga sun ce ‘Yan Bindigar sun shigo garin ne sanye da kakin Soja.
Hare haren dai na zuwa ne cikin dokar ta-baci da aka kafa a Jahohin Borno da Yobe da Adamawa domin farautar ‘Yan Boko Haram.

Inda Jami’an tsaron Najeriya ke ikirarin suna samun nasara akan ‘Yan Boko Haram, yayin da kuma a wani sakon Bidiyo Shugaban Kungiyar Imam Abubakar shekau ke ikirarin suna cikin koshin lafiya.

Akalla mutane sama da 3000 ne aka ce sun Mutu tun shekarar 2009 da aka fara rikicin Boko Haram a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.