Isa ga babban shafi
Masar

Hukumomi a Masar sun tabbatar da mutuwar mutane tara a harin da aka kai

Hukumomin kasar Masar, sun tabbatar da mutuwar mutane 9, a hare-haren da aka kai wa cibiyoyin jami’an tsaron kasar a jiya Litinin, lamarin da ya faru a daidai lokacin da magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammad Morsi ke neman ganin an sake dawowa da shi a kan karagar mulki.

Lokacin ana ganiyar rikicin kasar Masar
Lokacin ana ganiyar rikicin kasar Masar REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Kamar yadda ma’aikatar cikin gidan kasar ta tabbatar, da farko wata mota ce da aka makare ta da bama-bamai ta fashe a wajen ginin shalkwatar ‘yan sanda a kudancin yankin Sinai, inda mutane suka rasa rayukansu, sai kuma wasu ‘yan bindiga da suka bude wuta tare da kashe sojoji shida a kusa da Suez na yankin Isma’iliyya.

Hare haren dai sun faru ne kwana daya bayan da magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammad Morsi suka bukaci gudanar da zanga-zangar neman a dawo da shi a kan madafan iko, wato a ranar lahadi lokacin da ake tunawa da cika shekaru 40 da barkewar yaki tsakanin Isra’ila da kasashen larabawa.

Har ila yau a jiya Litinin wasu maharan sun harba manyan rokoki da suka fada kan cibiyar tauraron da ke bai wa al’ummar kasar damar yin kira ta wayar tarho zuwa sauran kasashen duniya da ke birnin Alkahira.

A jimilce dai mutane 51 ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankula da kuma hare haren da suka faru a kasar a cikin ‘yan kwanakin baya bayan nan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.