Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta Kudu

Mutanen yankin Abyei suna jefa kuri’ar raba gardama

Mutanen yankin Abyei mai arzikin Man Fetir da Sudan ke takaddama da Sudan ta Kudu sun fara jefa kuri’ar raba gardama domin tantance yankin da suke so takanin kasashen biyu. Mutanen yankin za su zabi Sudan ko Sudan ta Kudu domin kawo karshen rikicin da ake yi a yankin.

Mutanen yankin Abyei suna jefa kuri'ar zaben raba gardama akan yankin da suke so tsakanin Sudan da Sudan ta kudu.
Mutanen yankin Abyei suna jefa kuri'ar zaben raba gardama akan yankin da suke so tsakanin Sudan da Sudan ta kudu. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Dakarun wanzar da zaman lafiya ne na Majalisar Dinkin Duniya kimanin 4,000 ke kula da sha’anin tsaro a lokacin da al’ummar yankin ke kada kuri’a.

Tun a shekarar 2011 ne al’ummar yankin Abyei ya kamata su kada kuri’ar raba gardamar yankin da suke so karkashin yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla kafin ballewar yankin Kudanci a 2005.

A ranar Lahadi Tawagar Tarayyar Afrika ta nemi shiga yankin na Abyei amma kungiyar ta bayyana takaicinta saboda rashin samun kai wa ga yankin.

A wata Sanarwa, kungiyar ta Tarayyar Afrika ta zargi gwamnatin Sudan da haramta mata shiga yankin, saboda wasu dalilai da gwamnatin al Bashir ta bayar na tsaro.

Kwamitin zaman lafiya da tsaro ne na kungiyar ya nemi shiga yankin na Abyei , amma Kwamitin yace akwai bukatar kasashen Afrika su shiga tsakani domin kawo karshen takaddamar da ke tsakanin kasashen biyu game da yankin na Abyei.

Akwai dai ganawa da aka yi tsakanin al Bashir na Sudan da takwaransa na Kudu Salva kiir domin samun jituwa akan sabanin da ke tsakaninsu, amma kuma babu wani ci gaba da ganawar ta haifar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.