Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire-Japan

Japan ta tallafawa kasar Cote d’Ivoire a ziyarar Abe

Firaministan kasar Japan Shinzo Abe wanda a jiya juma’a ya isa birnin Abidjan na kasar Cote D’Ivoire, ya sanar da bai wa kasar tallafin kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka milyan 90 domin raya tattalin arzikinta.

Ziyarar Shinzo Abe da Côte d'Ivoire yana ganawa da Shugaba Alassane Ouattara
Ziyarar Shinzo Abe da Côte d'Ivoire yana ganawa da Shugaba Alassane Ouattara AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

A lokacin wannan ziyarar, Firaminista Abe na tare da rakiyar manyan ‘yan kasuwa da kuma masu masana’antu na kasar Japan wadanda ke da niyyar saka jari a cikin kasashe da dama na Afirka da zai ziyarta, da suka hada har da Mozambique da kuma Ethiopia.

Sai dai kafin ya bar birnin Abidjan, Firaministan na Japan da kuma mai masaukinsa Alassane Ouattara, za su jagorancin wani taro dangane da batutuwan tattalin arziki da saka jari tsakanin Japan da kuma kungiyar CEDEAO-ECOWAS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.