Isa ga babban shafi
Masar

An shiga rana ta biyu a zaben raba gardama a Masar

Al’ummar kasar Masar a yau ne ake sa ran zasu kammala kada kuri’ar zaben raba gardama akan sabon kundin tsarin mulki wanda ake ganin zai ba babban hafsan sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Sisi damar darewa saman shugabancin kasar wanda ya hambarar da Morsi.

Wata mata tana kada kuri'ar zaben raba gardama game da sabon kundin tsarin mulkin kasar Masar
Wata mata tana kada kuri'ar zaben raba gardama game da sabon kundin tsarin mulkin kasar Masar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

A ranar Farko an samu tashin hankali inda aka ruwaito mutuwar mutane 9 a birnin al Kahira amma a wasu yankunan kasar an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Gwamnatin Masar dai tana son mutanen kasar su amince da sabon kundin tsarin mulkin ne domin kawar da tsarin mulkin Morsi shugaban dimokuradiya na farko a kasar da aka tumbuke.

Magoya bayan jam’iyyar ‘yan uwa Musulmi sun kauracewa zaben wadanda gwamnatin kasar ta danganta a matsayin ‘Yan ta’adda tare da haramta ayyukansu.

Uwais Rafindadi dan Najeriya da ke karatu a al Kahira yace an samu karancin masu kada kuri’a.

Tun kafin bude runfunan zabe ne a ranar Talata wani bam ya tashi kusa da kotun al kahira amma babu wani ta’adi da harin ya haifar.

Amma an samu mutuwar mutane uku a garin Kerdasa da ke kudancin al kahira, sannan wasu mutane biyar sun mutu a yankin kudancin Masar sakamakon arangama tsakanin ‘Yan sanda da masu zanga-zanga, yawanci magoya bayan Mohammed Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.