Isa ga babban shafi
Masar

Kotu ta dage sauraren karar Mohamed Morsi zuwa wata mai zuwa

A kasar masar, yau wata kotu ta dage shari’ar da ake wa hambararren shugaban kasar Mohamed Morsi, har zuwa watan Fabrairu. Wannan shine karo na 2 da ake dage sauraren karar tsohon shugaban, da kugiyar masu kishin Islama, da aka kifar da gwamnatin shi a watan Juli.Tsohon shugaban na fuskantar tuhuma ne tare da wasu mutane 14, sai dai kadan daga cikin su aka kawo kotun dake zamanta a wata makarantar horas da jami’an ‘yan Sanda, da ke wajen birnin Alkahira a yau Laraba.Alkalin kotun Ahmed Sabry Youssef, ya bayyana cewa rashin kyan yanayi ne ya sa aka gagara dauko tsohon shugaban daga gidan yari, don fusakantar shari’a.Ana zargin Morsi da kisan ‘yan adawan da suka yi zanga zangar neman ya sauka daga mukamin shi, a watan Disamban shekarar 2012.Cikin watan Nuwamba aka fara gurfanar da Muhamad Morsi, inda ya sa kafa ya yi fatali da hurunin kotun wajen hukunta shi, don a cewar shi, har yanzu shine shugaban kasar Masar.Wasu magoya bayan Morsin sun yin zanga zangar adawa da gurfanar da tshon shugaban, a sassan birnin Alkahira a yau Talata, inda ma’aikatar harkokin cikin gida tace an kama mutane 17.Yanzu kotun ta tsaida ranar 1 ga watan Fabrairu mai zuwa, don ci gaba da sauraren karar. 

wasu magoya bayan Morsi na zanga-zanga
wasu magoya bayan Morsi na zanga-zanga
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.