Isa ga babban shafi
Masar

Ana ci gaba da kidayar kuri’un zaben Masar

Ana ci gaba da kidayar kuri’un zaben raba gardama a kasar Masar amma rahotanni sun ce sakamakon farko ya nuna masu zabe sun amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar, wanda zai tabbatar da tumbuke Morsi tare da ba shugaban rundunar sojin kasar, Janar Abdel Fatah al Sisi damar takarar shugabancin kasar.

Sojan Masar yana tsare da akwantin Kuri'un Zaben raba gardama akan Kundin tsarin Mulki da aka gudanar
Sojan Masar yana tsare da akwantin Kuri'un Zaben raba gardama akan Kundin tsarin Mulki da aka gudanar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Rahotanni sun ce kashi 90 na masu kada kuri’ar sun goyin bayan sabon kundin tsarin mulkin da sojin kasar suka rubuta wanda suka ce yana kunshe da ‘Yancin Mata da fadin albarkacin baki.

‘Yan Uwa musulmi dai sun kauracewa zaben amma wani babban Jami’in gudanar da zaben Nabil Salib ya fito a kafar Telebijin din kasar yana cewa an samu fitowar masu kada kuri’a fiye da zabukan baya, ba tare da ya bayar da alkalumma ba.

A ranar Farko da aka fara zaben an samu rikici amma a ranar Laraba an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Ma’aikatar cikin gida tace akalla mutane 444 aka cafke wadanda suka fito suna zanga-zanga don dagula ayyukan zaben.

Gwamnati tana neman mutanen Masar su amince da sabon tsarin ulkin don samun nasarar kawar da na gwamnatin Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.