Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

MDD ta nuna takaicin ta kan yadda ake kashe yara kanana a Tsakiyar Afrika

Hukumar dake kula da yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya, wato UNICEF, ta nuna takaicin game da yadda ake guntile wasu sassan jikin yara tare da halakasu a ricikin kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka gano wani kabari dauke da gawawwaki a wani sansanin tsoffin ‘yan tawaye.

Tambarin Majalisar Dinkin Duniya
Tambarin Majalisar Dinkin Duniya
Talla

Hukumar ta UNICEF ta nuna takaicin na ta ne, yayin da Darektan yankin Yamaci da Tsakiyar Afrika Manuel Fontaine ya ke bayani ga manema labarai.

A cewarsa, an halaka tare da raunata akalla yara sama da 100 cikin watanni biyu da suka gabata, yana mai nuni da cewa babu yadda kasa zata ci gaba a indan manyan mutane da suka mallaki hankalin kansu suna kashe kananan yara.

A yanzu haka Hukumar ta UNICEF ta ce irin halin da yara suka shiga a kasar ta Jamhuriyar Tsakiyar Afrika bai iya misaltuwa.

Wannan kuma na zuwa ne yayin da aka gano wani makeken kabari dauke da gawawwaki 13 a wani sasanin tsoffin ‘yan tawayen, wadadan suka kawar da gwamnati kasar a shekarar da ta gabata.

A halin da ake ciki yanzu, Faransa wacce ta raini Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, na gudanar da wani taron kwamitin tsaron kasar kan rikicin, wanda ya hada da shugaba Francois Hollande da wasu manyan ministocin Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.