Isa ga babban shafi
Masar

An kai wa Jami’an tsaro harin bam a Masar

Wasu jerin hare haren bama bamai guda biyu da aka kai a kusa da ginin Jami’ar birnin Al Kahira sun yi sanadin mutuwar wani Janar din ‘Yan sanda. Kuma ‘Yan sandan Masar sun ce hare haren sun raunata karamin minitan cikin gida da wasu ‘yan sanda guda 5.

Jami'an tsaro suna sintiri a kusa da Jami'ar Al Kahira da aka kai hare haren bama bamai a Masar
Jami'an tsaro suna sintiri a kusa da Jami'ar Al Kahira da aka kai hare haren bama bamai a Masar REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Hare haren bama bamai har guda uku ne aka kai a birnin Al kahira, kuma an kai Hare hare guda biyu ne a kusa da ginin Jami’ar al Kahira inda suka yi sanadin mutuwar wani Janar Din ‘Yan sanda Tarek al-Mergawi, tare da raunata karamin Ministan cikin gida da wasu ‘yan sanda guda 5.

Sai dai kuma Kamfanin Dillacin labaran kasar ta MENA yace hari na uku, bai haifar da wani ta’adi ba.

Wannan shi ne hari na farko da ake kai wa Jami’an Gwamnati da Jami’an tsaro a ci gaba da tashin hankalin da ake samu a Masar bayan hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi na ‘Yan uwa musulmi.

Hare haren kuma na zuwa ne duka mako guda da babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Sisi, wanda ya tunmuke Morsi ya bayyana tube kakinsa domin shiga takarar zaben shugaban kasa.

Kafofin yada labaran Masar sun ce akwai wani bom na hudu da aka kwance wanda aka dasa a kusa da Jami’ar alkahira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.