Isa ga babban shafi
Masar

Masar: Sisi ya tube Kakin Soji don shiga Takarar zabe

Shugaban rundunar sojin kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya yi murabus daga mukaminsa, tare da bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar inda kuma ya sha alwashin yaki da Ta’adanci.

Babban hafsan Sojin kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi
Babban hafsan Sojin kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Hakan na faruwa ne watanni Tara bayan da Sisi, wanda ya taba rike mukamin Ministan tsaron kasar, ya jagoranci hambarar da gwamnatin Muhammad Morsi a watan Yulin bara.

Kasar Masar na sa ran gudanar da zaben ne a watan Yunin wannan shekara, sai dai magoya bayan Morsi sun sha alwashin dagula lamurran gwamnati a kasar idan har ba a mayar da Morsi kan mukaminsa ba.

Mohammed Morsi shi ne shugaban dimukuradiya na farko a Masar, kuma tun lokacin da al-Sisi ya tumbuke shi, magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ke gudanar da zanga-zanga, lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane da dama.

Sisi ya fito ne a kafar Telebijin yana bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban Kasa, wanda ake gani shi ne yanzu mai karfin fada a ji a kasar Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.