Isa ga babban shafi
Masar

Sojin Masar sun karyata labarin Jaridar Kuwait akan Sisi

Rundunar Sojin kasar Masar tace Jaridar Kuwait ta fassara kalaman Babban kwamandan askarawan kasar Marshal Abdel Fatah al-Sisi ba daidai ba, bayan ta ruwaito yace zai tsaya takarar neman shugabancin kasar a zabe mai zuwa. A cewar rundunan Sojin Al-sisi yace zai bayyana wa al’ummar kasar Masar kudirin shi idan lokaci ya yi.

Babban Hafsan Sojin Masar Abdel Fattah al-Sisi
Babban Hafsan Sojin Masar Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/Stringer
Talla

Tun da farko wata jarida mai suna Al-seyassah da ake bugawa a kasar Kuwait ce ta ruwaito cewa al Sisi ya tabbatar da kudirin zai tsaya takarar shugaban kasa tare da cewa zai yi hakan ne domin karba kiran al’ummar kasar da suka bukace shi ya tsaya takara.

A watan Afrilu ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Masar kuma an dade ana jiran al Sisi ya fito ya bayyana kudirinsa na tsayawa takara wanda ya hambarar da gwamnatin dimokuradiya ta Mohammed Morsi na ‘Yan uwa musulmi.

“Ba zan yi watsi da kiran Mutane ba” kamar yadda Jaridar ta ruwaito Kwamandan Sojojin na Masar na cewa.

Wannan na zuwa ne duka mako guda da Majalisar koli ta Sojin Masar ta bayyana goyon bayanta da Al-Sisi akan neman ya tsaya takarar shugaban kasa wanda babu tantama ana ganin zai lashe zaben da gagarumin rinjaye.

Dole dai sai al-Sisi ya tube Kakin shi na Soja kafin a hukumance ya kasance dan takara.

Magoya bayan Sisi dai suna ganin Sisi ya fi cancanta ya jagoranci kasar Masar bayan kwashe shekaru sama da uku kasar na cikin rudani tun lokacin da aka kawar da gwamnatin Hosni Mubarak a shekarar 2011.

Masana masu lura da rikicin siyasar kasar Masar suna ganin hare hare da ake samu daga mayakan Jihadi, babbar barazana ce ga samun zaman lafiya mai dorewa a kasar Masar.

Tun lokacin da aka tumbuke gwamnatin Morsi sama da mutane 1,000 ne suka mutu yawancinsu magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.