Isa ga babban shafi
Masar

A watan Afrilu za’a gudanar da zaben shugaban kasa a Masar

Gwamnatin kasar Masar ta bayyana lokacin da za’a gudanar da zaben shugaban kasa inda ake hasashen Janar Sisi zai tsaya takara wanda ya hambarar da gwamnatin ‘Yan uwa musulmi ta Mohammed Morsi.

Magoya bayan Janar Abdel Fattah al-Sisi a wani gangamin goyon baya a dandalin Tahrir a birnin al Kahira
Magoya bayan Janar Abdel Fattah al-Sisi a wani gangamin goyon baya a dandalin Tahrir a birnin al Kahira Reuters
Talla

Wannan na zuwa ne a lokacin da Mayakan Jihadi suka yi ikirarin daukar alhakin kakkabo jirgin saman sojin kasar a mashigin ruwan Sinai, wanda ya kashe sojoji guda biyar.

Kungiyar Ansar Beit al Maqdis, wadda ta dauki alhakin hare hare da dama a cikin kasar, tace dakarunta ne suka harbo jirgin a karshen mako, sai dai hukumomin soji sun ce jirgin hadari ya yi.

Shugaban kasar Masar na riko Adly Mansour ne ya bayar da sanarwar jadawalin zaben kwana guda bayan mutane sama da arba’in sun mutu a wata arangama tsakanin magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi da kuma wadanda ke goyon bayan gwamnatin kasar mai ci.

Daruruwan mutane ne suka fito suna bayyana goyon bayansu ga babban hafsan Sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Sisi.

Ana sa ran Sisi zai fito ya bayyana kudirin shi na tsayawa takarar zaben shugaban kasa da za’a gudanar a watan Afrilu.

Jadawalin zaben yana cikin sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka zartar da ke nuna za'a yi zabukan ne daga tsakiyar watan Afrilu na wannan shekara.

Gwamnatin kasar da sojan suka dora tace zata mayar da da mulkin demokuradiya kafin karshen wannan shekara ta 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.