Isa ga babban shafi
Save the Children

Iyaye Mata sun fi shan wahala a Afrika

Wani rahoton da kungiyar kare hakkin mata da yara kanana mai suna Save the Children ta fitar, ya bayyana jerin sunayen wasu kasashen Afrika 10 da rayuwar iyaye Mata ke cikin mummunan hadari.

Wasu Mata da 'yayansu suna kokarin ficewa garin Grimari a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da ke fama da rikicin addini
Wasu Mata da 'yayansu suna kokarin ficewa garin Grimari a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da ke fama da rikicin addini REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Rahoton ya bayyana sunayen kasashen Cote d’Ivoire da Chadi da Najeriya da Saliyo da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a matsayin kasashen da uwa ke rayuwa a cikin halin kunci.

Har ila yau akwai kasashen Guinea Bissau da Mali da Nijar da Jamhuriyar dimokuradiyyar Congo da kuma Somaliya, a cewar rahoton da aka buga bayan share tsawon shekaru 15 ana gudanar da bincike kan halin da mata ke rayuwa a duniya.

Binciken an gudanar da shi ne a cikin kasashen duniya daban daban har guda 178, inda aka auna matsayin da mata ke da shi a fannin kiwon lafiya da ilimi da tattalin arziki da kuma rawar da suke takawa a fagen siyasa.

Save the Children ta ce a Afrika, mace daya daga cikin 27 ne ke mutuwa a lokacin da suke dauke da juna biyu, yayin da yaro daya daga cikin 7 ke rasuwa kafin cika shekaru 5 a duniya,

Yayin da kasashen Afirka suka mamaye matsayi na 1 har zuwa na 10 inda mata ke rayuwar wulakanci, rahoton na Save the Children ya zana sunayen wasu kasashen da mata ke rayuwa irin ta jin dadi da holewa da suka hada da Finland da Norway da Sweden da Holland da Denmark.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.