Isa ga babban shafi
Masar

Sisi ya samu nasara a zaben Masar

Rahotanni daga kasar Masar sun ce tsohon shugaban rundunar sojin kasar Masar Abdel Fatah Al Sisi ya samu gagarumar nasara a kuri’in da aka kidaya a zaben shugaban kasa da aka shafe kwanaki uku ana jefa Kuri’a.

Wata tana sumbatar hoton Abdel Fatah al Sisi Wanda ya lashe zaben shugabancin Masar
Wata tana sumbatar hoton Abdel Fatah al Sisi Wanda ya lashe zaben shugabancin Masar REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

Sakamakon farko ya nuna cewa akalla masu jefa kuri’a Miliyan 21 ne ko kashi 96.2 cikin kashi 100 suka zabi Abdel Fatah Al Sisi, mutumin da ya jagorancin hambararar da gwamnatin Muhammad Morsi na ‘Yan Uwa Musulmi.

A daya bangaren kuma abokin hamayyarsa Hamdeen Sabbahi ya samu kashi 3.8 ne kawai cikin kashi 100 na kuri’un da aka kada.

Rahotanni sun ce magoya bayan Sojan sun bazama saman titunan kasar suna murna dauke da tutar kasar hade da hotansa.

Dama dai akwai hasashen cewa Al Sisi shi zai lashe wannan zabe ganin yadda aka murkushe bangaren ‘yan adawa na ‘yan uwa musulmai.

Yanzu haka ana ci gaba da kidayar inda rahotanni ke nuna cewa an kammala kirga kuri’un tashoshin kidaya 312 cikin 352 a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.