Isa ga babban shafi
Masar

‘Yan sandan Masar sun cafke magoya bayan Morsi da dama

Jami’an tsaro a kasar Masar sun cafke magoya bayan hambararren shugaban kasar akalla 157 wadanda ke gudanar da zanga-zangar cika shekara daya da kifar da gwamnatinsu daga kan karagar mulki. A share tsawon yinin Alhamis ana bata-kashi tsakanin jami’an tsaron da kuma mazu tarzoma, inda aka yi amfani da hayaki mai sa kwalla da motocin ruwan zafi domin tarwatsa masu zanga-zanga.

'Yan Sanda suna arangama da magoya bayan Morsi a birnin Al Kahira
'Yan Sanda suna arangama da magoya bayan Morsi a birnin Al Kahira REUTERS/Al Youm Al Saabi Newspaper
Talla

An samu tashin wani bom kuma a birnin al Kahira lokacin da Jami’an tsaro ke arangama da masu zanga-zanga. Mutane Tara ne aka ruwaito sun jikkata.

Tun lokacin da Sojoji suka hambarar da Morsi a ranar 3 ga watan Yuli, gwamnatin Masar ta haramta ayyukan kungiyar ‘Yan uwa Musulmi a Masar.

Abdel Fatah al Sisi wanda ya hambarar da Morsi yanzu shi ne Shugaban dimokuradiya a Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.