Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Sojojin Burkina sun yi alkawalin mika mulki ga farar hula

Sojojin kasar Burkina Faso sun yi alkawalin mika mulki ga duk shugaban da ‘Yan siyasar kasar suka amince ya jagoranci kasar bayan zanga-zangar da ta yi awon gaba da Blaise Compaore. Yayin da Kungiyar Tarayyar Afrika ta ba Sojojin wa’adi daga nan zuwa mako biyu, su mika mulki ga Farar hula.

Zaman sulhu tsakanin 'Yan siyasa da Shugaban Sojan Burkina Isaac Zida, a Ouagadougou
Zaman sulhu tsakanin 'Yan siyasa da Shugaban Sojan Burkina Isaac Zida, a Ouagadougou AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Shugaban kwamitin sulhu na Kungiyar Tarayyar Afrika ya bukaci Sojojin Burkina Faso su mika mulki ga Farar Hula nan da mako biyu, ko su kakabawa kasar Takunkumi.

Sojojin sun kwace mulki ne bayan mutanen Burkina sun tursasawa Compaore yin murabus a zanga-zangar kin jininsa da suka kaddamar a makon jiya.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban Sojan Kanal Zida, Sojojin sun yi alkawalin mika mulki ga gwamnatin hadin kai idan ‘Yan siyasa sun sasanta kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.