Isa ga babban shafi
Masar

Sisi ya kare gwamnati bayan wanke Mubarak

Shugaban Masar Abdel Fatah Alsisi, wanda ke bayyana matsayinsa a game da hukuncin da ke wanke tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak daga laifufukan da ake zargin sa da aikatawa, ya ce kasar ba za ta taba komawa baya ba kamar dai yadda wasu ke zato.

Hosni Mubarak, Tsohon shugaban Masar
Hosni Mubarak, Tsohon shugaban Masar REUTERS/Stringer/Files
Talla

Da dama daga cikin al’ummar Masar dai na kallon Al sisi a matsayin wanda ke ci gaba da yin biyayya ga tsohon shugaban wanda boren al’umma ya kora daga mukaminsa a shekara ta 2011 kafin daga bisani kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai saboda samun sa da hannu wajen kashe masu boren nuna adawa da shi.

‘Yan adawa a kasar Masar sun zargi kotun kasar da nuna son kai bayan ta wanke Tsohon shugaban kasar.

A ranar Assabar ne Kotun ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa Mubakrak tare da wanke wasu manyan Jami’an gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.