Isa ga babban shafi
Saliyo

Mutane sama da Miliyan 2, za su yi zaman gida na dole a Saliyo

A kokarin da hukumomin Kasar Saliyo ke yi na dakile yaduwar Cutar Ebola, Kimanin Mutanem miliyan 2 da dubu 500 ne za’a tilastawa zaman gida na dole har tsawon kwanaki uku  

Jami'an yaki da Ebola
Jami'an yaki da Ebola AFP PHOTO KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Hukumomin Kasar sun bayyana cewa, Saboda rage yawan masu kamuwa da cutar a kowace rana ne, yasa suka dauki wannan matakin.

A baya chan, a kan sami har kusan mutun dari, wani zubin kasa da haka, a matasyin  sabbin kamuwa da cutar ta Ebola, kamar yadda Farfesa Monty Jones ya bayyanawa RFI kenan, kuma ya kara da cewa, yanzu ana samun kasa da mutane 16 dake kamuwa da cutar a kullum.

A dayan bangaren, Farfesa Jones ya sanar da bukatan hukumomin kasar Saliyo, inda yace, burinsu shine ganin an yi bankwana da cutar baki daya cikin kankanin lokaci.

Cutar Ebola, ta kashe mutane kimanin dubu 10 a kasashen Saliyo Liberia da Guinea, inda cutar ta fi kamari a duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.