Amurka na daukan matakan warware rikicin siyasar saliyo
Ma’aikatar Harkokin wajen Amurka tace tana daukar matakan da suka dace dan warware rikicin siyasar kasar Saliyo bayan da mataimakin shugaban kasar ya nemi mafakar siyasa a ofishin Jakadancin ta
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun ma’aikatar Darby Holladay, tace ya zuwa yanzu dai mataimakin shugaban kasar Saliyo Samuel Samsumana baya ofishin Jakadancin ta dake Freetown, inda tayi kira ga bangarorin siyasar kasar da suyi anfani da kundin tsarin mulkin kasar dan warware takaddamar.
Mataimakin shugaban kasar yace sojoji sun mamaye gidan sa a karshen mako bayan Jam’iyyar su ta APC ta kore shi saboda zargin tada hankali.
Ya zuwa yanzu dai ba’a san inda ya buya ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu