Isa ga babban shafi
Kenya

Ana Zanga-zangar neman cikakken tsaro a Kenya

Daruruwan mutanen Kenya yawancinsu dalibai sun fito suna zanga-zangar neman cikakken tsaro a yau Talata bayan mummunan harin da mayakan al Shabaab suka kai a Jami’ar garin Garissa inda suka kashe mutane 148.

Masu zanga-zangar adawa da kisan mutane 147 a kasar Kenya
Masu zanga-zangar adawa da kisan mutane 147 a kasar Kenya RFI/Sonia Rolley
Talla

An gudanar da zanga-zangar a birnin Nairobi da kuma garin Garissa inda Mayakan Al Shabaab suka kai hari.

Har yanzu Jami’an tsaro na ci gaba da farautar wadanda suka kai harin.

Kamfanin Dillacin Labaran Faransa ya ruwaito cewa daruruwan mutane, Musulmi da Kirista ne suka hada gangami a garin Garissa domin nuna adawa da harin.

A birnin Nairobi kuma dalibai da daman e suka fito saman titi suna zanga-zanga.

Gwamnatin kasar tace dakarunta sun tarwatsa sansanin mayakan al Shabaab a Somalia, amma al’ummar kasar na ci gaba da bayyana bacin ransu game da zargin  Jami’an tsaro akan sun samu gargadin za a kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.