Isa ga babban shafi
Kenya

Soji sun kai farmaki ga al-shabab a kasar Kenya

Sojojin kasar Kenya sun kaddamar da harin Sama akan sansanonin kungiyar Al-shabab, inda suka kona sansanin mayakan akalla 2 a wani wuri da ke kusa da iyakar kasar da kasar Somalia

Des soldats kenyans arrivent à l'université de Garissa, le 4 avril.
Des soldats kenyans arrivent à l'université de Garissa, le 4 avril. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Wannan dai shi ne karon farko da dakarun Kenya ke amfani da Jiragen yaki wajen yin luguden wuta a kan sansanonin al-shabab, bayan harin da aka kai wa jami’ar Garissa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 148.

Mai magana da yawun Dakarun sojin kasar David Obonyo ya sanar da cewar, sun kona sanssanin mayakan biyu, kuma za su cigaba da kai musu hari domin kawo karshen ayyukan kungiyar.

Lamarin kuma na zuwa ne bayan Shugaban kasar Kenya Uhurru Kenyatta ya sha alwashin daukar fansa, da kuma yaki da ta’adanci a kasar, bayan faruwar harin Garissa, da ya yi matukar haddasa tsoro a zukatan al’ummar kasar.

Kungiyar al-shabab dai ta yi barazanar cigaba da kai irin wannan hari a kasar, matukar dai Kenya ba ta janye dakarunta daga Somalia ba.

Ko a shekarar 2013 ma kungiyar ta kai makamancin wannan harin a wani katafaran kanti da ke Nairobi, harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 67.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.