Isa ga babban shafi
US-Kenya

Amurka zata karfafa dangantakar ta da Kenya

John Kerry sakataren harkokin wajen Amurka ya fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a Kenya inda ake sa ran zai tattauna da hukumomin kasar kan matsalar tsaro kafin ziyarar da shugaba Barack Obama zai kai kasar.

John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka
John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka AFP PHOTO/ Ishara S. KODIKARA
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen kasar tace Amurka na da kyaukyawar alaka da Kenya wadda ta zarce shekaru 50, tareda taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma al’adun ta.
Ana saran Kerry ya tattauna da Kenyatta kan yadda za’a kawo karshen hare haren kungiyar Al Shebaab dake cigaba da karuwa a kasar.
Bayan ziyarar Kerry ana saran shugaba Barack Obama zai ziyarci kasar.
A Karon farko shugaban kasar Amurka Barack Obama ya shirya kai ziyara kasar Kenya a watan Yuli inda mahaifinsa ya fito, kuma ana saran zai kai ziyara kauyensu.

Fadar shugaban tace Obama a lokacin ziyarar zai halarci wani taron da zai taimakawa matasa dogaro da kan su kafin ya gana da shugaba Uhuru Kenyatta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.