20 ga watan Yuni ranar yan gudun hijira a Duniya
A yau assabar 20 ga watan Yuni, Majalisar Dimkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘Yan gudun hijira ta duniya, ranar da kan mayar da hankali a kan yadda za a iya inganta rayuwar miliyoyin mutane da ake musgunawa, tashin hankali, yaki da kuma cin zarafin Bil Adama ya tilastawa tserewa daga gidajen su.
Wallafawa ranar:
Ranar a bana na zuwa ne, a daidai lokacin da Hukumar Kula da Yan gudun hijira ke cewa akalla mutane miliyan 60 ne ke gudun hijira sakamakon tashe tahsen hankulan da aka samu a shekarar 2014, wanda hakan ya nuna karuwar kusan miliyan 8 da rabi kan na shekarar 2013, kuma sama da rabin mutanen yara ne kanana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu