Isa ga babban shafi
Liberia

Ebola ta sake yin kisa a Liberia

A Liberia an sake samun mutuwar mutum na biyu da cutar Ebola ta kashe, yayin da adadin wadanda ke dauke da cutar suka kai kimanin mutane shida bayan an yi bankwana da cutar a watanni biyu da suka gabata.

Cutar Ebola ta dawo Liberia bayan an yi bankwana da cutar
Cutar Ebola ta dawo Liberia bayan an yi bankwana da cutar AFP PHOTO / ZOOM DOSSO
Talla

Yanzu dai Ana fargabar Ebola na iya ci gaba da yaduwa a Liberia, duk da mahukunatan kasar sun ce suna daukar matakan gaggawa.

Wata mata ce mai suna Kebbeh Kolie ta mutu jim kadan bayan an kwantar da ita a asibiti bayan ta kamu da cutar Ebola.

Kuma matar ta kamu da cutar ne daga wata ‘yar uwarta a yankin Margibi inda aka sake samun bullar Ebola kusa da birnin Monrovia.

Yanzu dai ita ce mutum ta biyu da ta mutu sakamakon Ebola tun bayan warkar da cutar baki daya a watan jiya.

Yanzu kuma al’ummar Liberia na cikin fargaba akan cutar na iya ci gaba da yaduwa, musamman a yankin da cutar ta bulla da ke kusa da babban birnin kasar.

Sama da mutane dubu 11 suka mutu tun barkewar ebola a Liberia a karshen 2013.
A ranar 9 ga watan Mayu ne Liberia ta bayyana yin bankwana da cutar mai yin kisa amma kuma yanzu sai gashi cutar ta dawo a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.