shugaba Obama na shirin soma ziyarar aiki a kasar Kenya
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya sanar cewa ziyarar da shugaba Barack Obama zai kai a kasar ta kenya a ranar juma’a mai zuwa mai matukar mahinmancin ne kwarai, inda ya yi watsi da batun auren jinsi guda daga cikin batutuwan da zasu tattauna.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar ta kenya Uhuru Kenyatta yace babu batun kare hakkin masu auren jinsi guda, a cikin abubuwan da za su a tattauna da shugaba Obama.
Shugaban yace Kenya, da ma Nahiyar Africa nada batutuwa masu muhimmanci dake bukatar a baiwa mahinmanci a tattauna da hukumomin Amurka, da suka kunshi sauran kasar da suke hulda da ita.
Kenyatta ya kuma yi karin haske a kan batun mataimakinsa William Ruto, da kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya ICC ke tuhuma bisa zargin tayar da rikici bayan zabe a shekara ta 2007, kuma shi ma zai gana da shugaban na Amurka a yayin wannan ziyarar.
Kasar kenya dai ita ce asalin mahaifin shugaban na Amurka Barack Obama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu