Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Dakarun Sudan ta kudu sun kona fararen hula da ransu- HRW

Hukumar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi dakarun gwamnatin Sudan ta kudu da kashe farare hula da dama tare da kona wasu da ransu da yi wa mata fayde a yayin da suke kokarin tsere wa rikicin kasar.

Sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da ke fada da 'Yan tawayen Riek Machar
Sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da ke fada da 'Yan tawayen Riek Machar REUTERS
Talla

A cikin rahoton hukumar na tabargazar da dakarun Sudan suka aikata tace da gangan Sojojin kasar ke kai wa Fararen hula hari, al’ amarin da ta bayyana a matsayin laifukan yaki.

Rahoton hukumar ta ce dakarun na bin mutane da gudu da tankar yaki, tare da take su har sai sun tattabar da sun mutu.

Hukumar HRW ta wallafa rahoton ne bayan ta zanta da wasu al’ummar kasar da Mata da aka yi wa fayde wadanda suka tsira daga dakarun gwamnatin Sudan ta kudu da kuma mayakan sa-kai ‘Yan kabilar Nuer da ke mara masu baya.

Rikicin Sudan ta kudu dai ya barke ne a watan Disemban 2013 bayan Shugaban kasar Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Reik Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.