Isa ga babban shafi
Saliyo

Saliyo za ta sake gina tattalin arzikinta bayan kawar da Ebola

Shugaban kasar Sierra-Leone Ernest Bai Koroma, ya sanar da wani sabon shiri domin sake gina kasar bayan share tsawon fiye da shekara daya tana fama da cutar Ebola, lamarin da ya yi matukar shafar tattalin arziki da kuma sauran bangarori na rayuwar jama’a.

Shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma
Shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma Reuters/Thierry Gouegnon
Talla

A wata sanarwa da ta fitar, fadar shugaba Ernest Bai Koroma, ta bayyana cewa wannan shiri za a a aiwatar da shi ne a cikin shekaru biyu masu zuwa da nufin sake farfado da tattalin arzikin kasar a matakin farko, wannan kuwa ta hanyar karfafawa kamfanoni masu zaman kansu da kirikiro da sabbin gurabobin ayyukan yi da kuma inganta rayuwar al’umma.

Hakazalika gwmanati za ta yi kokarin samar da makamashi da ruwa mai tsafta a wadace ga al’ummar kasar, kuma ana bukatar akalla dalar Amurka milyan 804 tare da samun tallafin Majalisar Dinkin Duniya, kamar dai yadda aka tsayar a lokacin wani taro a Majalisar ta dauki nauyi kan yadda za a taimaka wa kasashen da cutar Ebola ta shafa.

Kasashen duniya dai sun yi alkawalin samar da kudaden da yawansu zai kai dala bilyan uku da milyan 400 domin sake gina kasashe uku da cutar ta shafa, wato Saliyo da Liberia da kuma Guinea-Conakry.

Cutar dai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 11, tare da haddasa mummunar illa ga tattalin arzikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.