Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kashe mutane 9 a wasu kauyukan Jihar Yobe

Mayakan Boko Haram sun harbe mutane 9 tare da cinna wa gidaje wuta a jerin hare hare da suka kaddamar a wasu kauyukan jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Yanzu 'Yan Boko Haram na bin salon abkawa gari su kona gidaje tare da wawushe dukiyoyin Jama'a
Yanzu 'Yan Boko Haram na bin salon abkawa gari su kona gidaje tare da wawushe dukiyoyin Jama'a AFP PHOTO/AMINU ABUBAKAR
Talla

Mayakan na Boko Haram sun shiga kauyukan ne guda biyu Tadagara da Dunbulwa saman babur a ranar Laraba da dare inda suka kama harbi har wajewar gari, kamar yadda wasu mazauna yankin suka tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa.

‘Yan bindigar kuma sun kona gidaje tare da wawushe dukiyoyin jama’a.

Wasu da mazauna garin da suka tsere cikin daji sun ce suna ganin yadda gidajensu ke cin wuta.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan Boko Haram sun yanka wuyan mutane 10 masu sana’ar kamun kifi a kusa da Baga a makon jiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.