Isa ga babban shafi
Amurka-Najeriya

Amurka za ta sayar wa Najeriya da makamai

Amurka ta amince ta sayarwa da Najeriya Makamai domin yaki da Mayakan Boko Haram da ke addabar kasashen yammacin Afrika da ke kewaye da tafkin Chadi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da Barack Obama na Amurka a ziyarar da ya kai a Washington
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da Barack Obama na Amurka a ziyarar da ya kai a Washington REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Wata tawagar ‘Yan Majalisun Amurka da suka kawo ziyara a Najeriya sun bayyana cewar Amurka za ta taimakawa Najeriya da makaman da ta ke bukata domin fuskantar kungiyar Boko Haram.

Shugaban tawagar Darell Issa, Dan jam’iyyar Republican ya bukaci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gaggauta magance matsalar cin zarafin Bil Adama da ake zargin wasu jami’an tsaron kasar.

Hakan dai na nufin Amurka za ta janye takunkumin da ta kakabawa Najeriya karkashin wata doka ta ‘Yancin bil’adama saboda zargin keta hakkin bil’adama da ake zargin Sojojin Najeriya da aikatawa a yakin da suke da Boko Haram.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya jagoranci tawagar ‘Yan Majalisu domin ganewa idonsu halin da mutanen yankin arewa maso gabashin kasar su ke ciki wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.