Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Amnesty na son a dakatar da ‘Yan sandan da suka yi kisa a Marikana

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta dakatar da ‘Yan sandan kasar da suka taka-rawa wajen kashe ma’aikatan mahar ma’adinan kasar 34 har zuwa lokacin da aka kammala bincike akan lamarin.

'Yan mutanen da aka kashe a Marikana zuna kallon Jawabin shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma
'Yan mutanen da aka kashe a Marikana zuna kallon Jawabin shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma AFP PHOTO / GORDON HARNOLS
Talla

Kungiyar ta kuma bukaci fadada matakin har zuwa kan wadanda suka nemi hana gudanar da binciken.

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar ta bukaci shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya dakatar da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan kasar Riah Piyega, saboda yadda aka kwashe shekaru 3 ba tare da an hukunta koda jami’i guda ba cikin wadanda suka aikata kisan.

Kungiyar ta ce yadda ‘Yan Sandan suka hada kansu suna kyamatar rahotan kwamitin binciken Farlam, ya dace shugaba Zuma ya nuna dattako da shugabanci na gari wajen hukunta manyan jami’an ‘Yan Sandan, a cewar Deprose Muchena, Jami’ar Amnesty a kudancin Afirka.

Muchena tace rashin daukar matakin zai zama rashin hukunta wadanda suka aikata kisan kai da gangan ranar 16 ga watan Agusta na shekarar 2012 da kuma rashin adalci a bangaren shari’a.

Kungiyar ta kuma bukaci biyan diyya ga iyalan ma’aikatan da aka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.