Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu ta dage zaman sulhu bayan baraka a tsakanin 'yan tawaye

Gwamnati a kasar Sudan ta Kudu ta sanar da dakatar da duk wani batu na tattaunawa sakamakon rarrabuwar kawuna da aka samu a tsakanin ‘yan tawayen kasar, wannan kuwa duk da barazanar takunkumi da kasar ke fuskanta daga wasu kasashen duniya.

Riek Machar da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Riek Machar da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

A yau juma’a gwamnatin kasar ta Sudan ta Kudu ta fitar da sanarwar janyewa daga zaman da aka shirya domin ganin an kawo karshen yakin basasa na tsawon watanni 20.

Acewar wani wakilin gwamnati Loius Lobong bayan ganawa da shugaba Salva Kiir ya ce matakin ya zama dole kuma zai kasance haka har sai bangarorin ‘yan tawaye sun iya warware sabanin dake tsakaninsu.

A ranar talata da ta gabata ne dai ‘yan tawayen da ke goyon bayan Riek Machar suk sanar da janye goyon bayansu bayan sun zargi Machar da nuna son kai a fafutukar samun mulkin kasar da yake yi, saboda haka ‘Yan tawayen sun ce baza su amince da duk wani yarjejeniya da aka kulla da shi ba.

Yanzu haka kasar na fuskantar barazana daga wasu kasashen duniya na kakkaba mata takunkumi sakamakon kasa cimma matsaya na sulhu a kokarin kawo karshen tashe tashen hankulan da ya hallaka dubban mutane tare da tilastawa miliyoyi tserewa daga gidajen su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.