Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Salva Kiir zai hallarci zaman Sulhu a Addis ababa

A yau lahadi ake saran Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir zai hallarci zaman tattaunawar Sulhu da ‘yan tawayen kasar da ake gudanarwa a birnin addis ababa na kasar Habasha.Sakamakon a baya da ya ce ba zai hallarci zaman ba.

shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir Reuters/Goran Tomasevic
Talla

Sanar da wannan sabon sauyin na zuwa ne, kwana guda bayan Salva kiir  ya ce ba zai hallarci zaman tattaunawar ba, sai dai kuma ana gani cewar rashin hallatar zai  sa aka sa cim ma matsaya.

Kasar sudan ta kudu da ‘yan tawayen na fuskantar matsalin lamba daga kasashen da dama na cimma matsayar sulhu kafin 17 ga watan Augusta nan domin kawo karshan yankin basasar kasar da ke lakume rayukan duban’yan kasar.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne gwamnatin kasar  Sudan ta Kudu ta fitar da sanarwar janyewa daga zaman da aka shirya domin ganin an kawo karshen yakin basasa na tsawon watanni 20.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.