Isa ga babban shafi
Kenya-China

Kenya ta kulla yarjejeniya da China kan makamashin Nukiliya

Kasar Kenya ta sanya hannu kan yarjejeniyar gina cibiyoyin lantarki ta hanyar makamashin nukiliya tsakaninta da kasar China domin aikin inganta wutar lantarki a kasar daga nan zuwa shekara ta 2025.

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Talla

Wannan kuma na zuwa ne bayan Kenya ta kulla irin wannan yarjejeniyar da Korea ta kudu da kuma Slovakia

Kenya na kokarin samar da babbar cibiyar lantarki ta hanyar makamashin nukiliya da nufin samar da karfin wuta MW 1000 daga nan zuwa 2025 tare da inganta tsarin zuwa MW 4000 a 2033.

Karkashin yarjejeniyar, China za ta samar da horo na musamman ga ‘Yan Kenya a fannin nukiliya.

Tuni Kenya ta kulla irin wannan yarjejeniyar da Korea ta Kudu kuma dalibai da dama ne aka tura kasa domin samu ilimi a fannin gina lantarki ta hanyar makamashin Nukiliya.

Bankin Duniya ya ce cikin mutane 10 a Kenya 3 daga cikinsu na samun lantarki, amma adadin ya ragu zuwa biyu cikin 10 a yankunan karkara.
Yanzu bukatar lantarkin na dada karuwa musamman saboda karuwar yawan al’umma.

Amma Kenya ta fuskanci fari wanda ke haifar da tarnaki ga bukatar kasar na bnkasa gina cibiyoyin lantarki ta hanyar makamashin nukiliya

Karancin lantarki dai na cikin manyan matsalolin da ke haifar da koma-baya ga kasashen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.