Isa ga babban shafi
Faransa-Congo

Kotu ta bada umarni kwace kadarorin Iyalan Nguesso

Wata Kotu a kasar Faransa ta bada umurnin kwace wasu kadarorin da iyalan shugaban kasar Congo Dennis Sassou Nguesso suka mallaka a wani bincike na mallakar dunkiyar sata da ake musu.

Shugaban kasar Congo Denis-Sassou Nguesso
Shugaban kasar Congo Denis-Sassou Nguesso AFP/Thierry Carlier
Talla

Shugaba Sassou Nguesso na daga cikin shugabannin kasashen Afirka da ake zargi da rub da ciki da kudaden talakawan kasar su, ta hanyar sace dukiyar suna sayen kadarori a Turai.

Kasar Faransa ta kaddamar da bincike kan irin wadannan shugabanni a shekarar 2008 kuma ya zuwa yanzu an ritsa da shugaba Teodoro Obiang Nguema na Equatorial Guinea da marigayi shugaba Omar Bongo na Gabon da dan sa Ali Bongo mai shugabancin kasar yanzu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.