Isa ga babban shafi
Congo

Nguesso ya tube ministocin da ke adawa da canza kundin tsarin mulkin Congo

Shugaban Kasar Congo Brazzaville Dennis Sassou Nguesso ya yi garambawul ga majalisar ministocinsa inda ya kori biyu daga cikin wadanda ke adawa da sauya kundin tsarin mulkin don ba shi damar  sake neman wa’adin shugabanci a kasar.

Shugaban Kasar Congo Brazzaville Dennis Sassou Nguesso
Shugaban Kasar Congo Brazzaville Dennis Sassou Nguesso AFP PHOTO / THIERRY CHARLIER
Talla

Ministocin da aka kora sun hada da Claudine Munari na kasuwanci da Guy Brice Parfait Kolelas na ayyukan gwamnati kamar yadda gidan radion kasar ya sanar yau Talata.

A watan da ya gabata ministocin biyu sun shiga jerin gwanon ‘yan adawa domin bayyana rashin amincewarsu da shirin sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Taron kasa da shugaban ya hada ya amince da gagarumin rinjaye kan kudirin gyara kundin tsarin mulkin kasar.

Cire adadin shekarun Dan takarar kujerar shugaban kasa da wa’adin shugabanci na daga cikin gyare gyaren da aka yi wa Kundin tsarin mulkin kasar.

Sassou Nguesso ya taba zama shugaban kasa a jamhuriya ta farko lokacin da ana bin tsarin Jam’iyya guda a 1979 amma ya sha kaye a lokacin da aka fara bin tsarin Jam’iyyu a zaben kasar da aka gudanar a 1992.

Nguesso ya sake darewa kan madafan iko a 1997 bayan kammala yakin basasa a kasar, sannan an sake zabensa a 2002 da 2009, kuma yanzu yana neman zarcewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.