Libya
Kwamandojin 'yan tawaye sun mutu a hatsarin jirgin saman Libya
Wani jirgi mai saukar angulu dauke da mutane 23 ya fado a kusa da birnin Tripoli na kasar Libya to sai dai kawo yanzu babu cikakkun bayanai a game da dalilan wannan hatsari.
Wallafawa ranar:
Talla
Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 9, yayin da bayanai ke nuni da cewa da dama daga cikin wadanda ke cikin jirgin manyan kwamandojin ‘yan tawayen da ke mamaye da birnin Tripoli ne.
Libya dai kasa ce da ke fama da rikici tun a shekara ta 2011 lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban kasar Mu’ammar Kaddafi, kuma tun a wannan lokaci ba wata karbabbiyar gwamnati a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu