Isa ga babban shafi
Rwanda

Rwanda za ta kada kuri'ar sauya kundinta

Yau ake sa ran Majalisar kasar Rwanda za ta kada kuri’ar amince wa da sauya kundin tsarin mulki domin bai wa shugaba Paul Kagame damar sake tsaya wa takara a karo na uku.

Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame.
Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame. REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Majalisar ta tafka mahawara a jiya Laraba sakamakon kudirin da magoya bayan shugaban sama da miliyan uku da rabi su ka gabatar, inda su ka bukaci sauyin saboda abinda su ka kira irin ayyukan ci gaba da shugaban ke yi wa kasar.

Idan Majalisar ta amince da kudirin za a bai wa al’ummar kasar damar jefa kuri’a a zaben raba gardama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.